Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya sake fitowa a wani hoton bidiyo inda ya ke ikirarin daukar alhakin hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Maiduguri Jihar Borno.

A cikin sakon bidiyon, shekau ya ce sun gwabza fada da sojoji a kan iyakar kamaru tare da karyata ikirarin gwamnatin kasar da ta ce ta kashe mayakan shi 60 cafke wasu 20 da kuma kubutar da mutane sama da 5,000 a makwannin da suka gabata.

A hoton bidiyon na tsawon minti 27 , shugaban na Boko Haram ya ce yana nan garau tare da karyata ikirarin an raunana shi.

Sai dai kuma yanayinsa da babatunsa ba kamar yadda ya saba ba, a hoton bidiyon da ya fito tare mayakansa biyu a bayansa sun rufe fuska rike da makami.

Wannan ne karon farko da shekau ya fito tun fitowarsa a hoton bidiyo a watan Disemban bara lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun kakkabe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky