Sayyid Nasrullah: Majalisar Dinkin Duniya Ba Abin Dogaro Ba Ce

Sayyid Nasrullah: Majalisar Dinkin Duniya Ba Abin Dogaro Ba Ce

Babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah, ya bayyana majalisar dinkin duniya a matsayin wata kaskantacciyar cibiya da ba ta da 'yanci na kashin kanta, a kan haka ba abin dogaro ba ce kan warware matsalolin da suka addabi kasashen musulmi da ma na duniya.

Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da zagayowar lokacin haihuwar Sayyidah Fatima Zahra (AS) diyar amnzon Allah (SAW) a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Ya ci gaba da cewa nuna gazawar da MDD ta yi kan rahoton da ke tabbatar da cewa Isra'ila daula ce ta wariya, hakan shi kadai babban dalili ne da ke tabbatar da rauni da kuma kaskancin da MDD take ciki, kuma ba za ta iya tabuka komai ba domin kwato hakkin Palastinawa.

Dangane da rikice-rikicen da ake fama da su a kasashen larabawa kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen larabawa ne da kansu suke daukar nauyin hakan domin kare manufofin Amurka da Isra'ila, inda ya bayar da misali da abin da ke faruwa a Syria, inda tun daga lokacin da 'yan ta'adda suka fara kai hari a Syria shekaru 6 a jere, duk da dukiyar larabawa ake daukar nauyin wannan ta'addanci, ya ce; da a ce kudin da Saudiyya ta kashe wajen daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria cikin shekaru 6, za a yi amfani  da su a kasashen larabawa, da an kawo karshen talauci a wadannan kasashen baki daya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky