Sayyid Ali khamna'i Ya ce Makirce-Makircen Amruka Ba Zaiyi Tasiriba Ga Iran

Sayyid Ali khamna'i Ya ce Makirce-Makircen Amruka Ba Zaiyi Tasiriba Ga Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Tsayin dakar jami'an Iran a kan hakkin da ya rataya a wuyarsu dangane da yarjejeniyar nukiliyar kasar lamari ne da zai kunyata Amurka tare da rusa makircinta.

A jawabinsa ga manyan jami'an gwamnatin Iran a yammacin jiya Laraba: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khamene'i ya jaddada cewa: Makomar shugaban kasar Amurka Donald Trump bata da bambanci da irin na wadanda suka mabace shi musamman George .W. Bush da Ronald Reagan, inda tarihi ya yi awungaba da su.

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kuma jaddada cewa ficewar kasar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da kasar Iran ta saba kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231, sannan ya jaddada yin kira ga kasashen Turai kan kada su kuskura su gabatar da kuduri a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan ficewar Amurka daga yarjejeniyar domin zata hau kan kujerar naki.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jaddada yi kira ga jami'an Iran kan daukan matakan da suka dace wajen kalubalantar bakar siyasar Amurka tare da matsa kaimi a fagen inganta harkar tattalin arzikin Iran da nufin kyautata rayuwar al'ummar kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky