Sayyid Ali Khamenei Ya Aike Da Taimakon Makudan Kudade Ga Musulmin Rohingya

Sayyid Ali Khamenei Ya Aike Da Taimakon Makudan Kudade Ga Musulmin Rohingya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ware makudan kudaden da suka kai dala dubu 250 don taimakawa 'yan gudun hijiran musulman Rohingya na kasar Myammar don rage musu irin wahalhalun da suke ciki sakamakon ci gaba da kisan kiyashin da ake musu a kasar.

A wata sanarwa da ofishin Jagoran ya fitar ya bayyana cewar bisa wasikar da shugaba kuma wakilin Jagoran a kungiyar Agaji ta Red Crescent ta Iran ya aika wa Jagoran juyin juya halin Musuluncin dangane da mawuyacin halin da musulmin Rohingyan suke jiki, Ayatullah Khamenei ya ware kudaden da suka kai Dala 250,000 (sama da Naira miliyan casa'in) a matsayin taimakonsa ga musulmin Rohingyan.

A baya ma dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya nuna tsananin damuwarsa dangane da halin da musulmin na Rohingya, wadanda suke fuskantar kisan kiyashi daga wajen sojojin gwamnati da dan daba mabiya addinin Buddha na kasar Myammar, suke ciki inda ya bukaci kungiyoyi da kasashen musulmi da su sauke nauyin da ke wuyan kan al'ummar musulmin Rohingyan.

A cikin wasikar da ya aike wa Jagoran, shugaban kungiyar Red Crescent ta Iran din yayi bayanin irin mawuyacin halin da musulmin na Rohingya suke ciki da kuma irin taimakon da kungiyar tasa ta ba su, yana mai kara bayanin cewa lalle akwai bukatar karin taimakon don rage wa musulmin wahalar da suke ciki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky