Saudiyya Ta Kori Wasu Manyan Hafsoshin ta Na Soji

 Saudiyya Ta Kori Wasu Manyan Hafsoshin ta Na Soji

Sarki Salman na Saudiyya ya sallami wasu manyan jami'an sojin kasar, ciki har da babban hafsan sojin kasar, Janar Abdel Rahmane ben Saleh al-Bunyan.

Tuni kuma aka maye gurbinsa da Laftana Janar Fayyad al-Ruwaili. 

An kuma sallami babban hafsan sojin sama da kuma na kasa.

Sanarwar da kamfanin dillancin labaren kasar ya fitar, ta ce an tura jami'an ne ritaya.

Wannan matakin dai na zuwa a daidai lokacin da yakin da kasar ke jagoranta a kasar Yemen yaki ci yaki cinyewa. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky