Saudiyya Ta Kai Hari Kan Masu Bikin Aure A Yemen

Saudiyya Ta Kai Hari Kan Masu Bikin Aure A Yemen

Rahotanni daga Yemen na cewa a kalla mutane 20 ne dake halartar wani bikin aure, suka gamu da ajalisu, biyo bayan wani harin sama.

Lamarin dai ya auke ne yammacin Jiya Lahadi a lardin Bani Qais, dake Hajja, a yankin arewa maso yammacin kasar ta Yemen, a cewar majiyoyin agaji.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai, wasu mutane 40 da aka garzaya dasu asibitin yankin sakamakon raunana da suka samu a cewar kungiyar agaji ta ''Médecins sans frontières'' a shafinta na Twitter.

Tuni dai 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis dake rike da ikon yankin, suka danganta hare-haren ga kawancen sojin kasa da kasa da Saudiyya ke jagoranta kan yakin kasar ta Yemen.Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky