Saudiyya : Hakkin 'Yan Isra'ila Ne Su Samu Kasa_ Ben Salman

Saudiyya : Hakkin 'Yan Isra'ila Ne Su Samu Kasa_ Ben Salman

Yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, Muhammad Ben Salman, ya ce hakkin 'yan isra'ila ne su mallaki kasarsu.

Ben Salman na bayyana hakan ne a wata hira da mujallar Atlantic ta Amurka inda ya ke ci gaba da ziyara, inda yacce  'yan Israila da Palasdinawa kowane na da 'yanci akan kasarsu.

Wannan dai wata manuniya ce ta kara dasawa tsakanin mahukuntan na yahudawa 'yan mamaya na Isra'ila da kuma Saudiyya.

A hukumance dai Saudiyya ba ta amince da kasar Israila ba, sai dai ana  samun kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu ta bayan shage.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky