Sanarwar Sojojin Iran: H.K.Isra'ila Ta Kusa Kawo Karshe

Sanarwar Sojojin Iran: H.K.Isra'ila Ta Kusa Kawo Karshe

Rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar nan ba da jimawa ba duniya za ta shaidi faduwa da kuma karshen haramtacciyar kasar Isra'ila.

Rundunar sojin na Iran ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan don tunawa da zagayowar Ranar Kudus ta duniya da za a  gudanar a ranar Juma'an nan mai zuwa inda ta bayyana cewar Ranar Kudus ta duniya wata alama ce da ke nuni da bayyanar gaskiya don tinkarar karya, kamar yadda kuma take nuni da hadin kan al'ummar musulmi wajen nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da kuma fada da sahyoniyawa da Amurka.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu dai haramtacciyar kasar Isra'ila ta zama saniyar ware sakamakon shan kashin da kungiyoyin ta'addancin da aka kirkira da nufin taimaka mata, hakan ne ma  ya sanya ci gaba da aikata danyen aikin da take aikatawa wanda ba abin da haifar mata face kawo karshenta.

A jibi Juma'a ne dai ake sa ran za a gudanar da Ranar Kudus ta duniya a nan Iran da ma wasu kasashen musulmi don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu kamar yadda marigayi Imam Khumaini (r.a) ya bukata wajen sanya juma'ar karshe na watan Ramalana a matsayin Ranar Kudus ta duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky