SANARWAR MANEMA LABARAI DA GA HARKAR MUSULUNCI

SANARWAR MANEMA LABARAI DA GA HARKAR MUSULUNCI

Bacewar tilas: Dole Sojoji su bayyana gaskiya, maimakon murguda rahotanni

Akwai labarin da ya mamaye mafi yawan kafafen sadarwa a farkon makon nan da ya yi kokarin boye gaskiyar Sanarwar Manema Labarai wadda Amnesty International ta fitar a matsayin wani bangare na ayyukan raya ranar wadanda aka tilasta bacewarsu ta duniya.
Duk da bayanin da Kungiyar Amnesty International ta fitar a bayyane yake kuma a sarari, amma sai ga shi labaran da kafafen sadarwar suka fitar suna kokarin murguda abin da Amnesty ta fada kuma take bukata. Hakika babu tantama, ‘yan koren jami’an tsaro na Sojoji ne da ke cikin ‘yan Jarida ke aikata irin wannan lamari.
Sun cuccusa wadansu kalmomi da jumloli na wawitarwa da kuma wadansu kalamai wadanda ba su daga cikin abin da Amnesty ta sanya a cikin rubutunta a kokarinsu na ganin sun wofintar da kuma canza manufar abin da ake son cimmawa. Duk wani zancen, “Malami mai tsattsauran ra’ayi” da kuma “IMN tana cikin rikici da gwamnati tsawon shekaru” bayanai ne na karya wadanda ‘yan koren da aka yi hayar su suka sanya da nufin kawar da fahimtar sakon wannan rana ta wadanda aka tilasta bacewarsu.
Domin kawar da duk wani shakku, Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci a Najeriya babu daya daga cikin su da ke fada da kowane irin mutum. Shaikh Zakzaky yana jagorantar wata Hark ace ta jama’a da tsallake shamakin da ke tsakanin kabilun da ke zaune a sassanin Najeriya da kuma yin kira a kan biyayya ga dokokin Allah. Idan da a ce lamari ne na “tsattsauran ra’ayi” ko “Rikici” da kuma tashin hankali, ta yaya zai samu irin wannan dimbin magoya baya da yake da su duk kuwa da irin mummunan mataki na karfi da mahukunta suke dauka a kan sa. Wanda kuma lallai wannan ne ya sanya mahukunta suke gallaza wa wannan Harka ta Musulunci.
Abin da ya kamata gwamnati da jami’an tsaronta su fuskanta a wannan muhimmin lokaci shi ne su fito su bayyana abin da suka yi dangane da daruruwan wadanda suka tilasta bacewar su da Amnesty take bayyanawa. Mun gabatar da dukkanin hujjoji wadanda suka hada da Sunaye, hotuna, shekaru, hanyoyin ganawa da danginsu da kuma wuri da lokaci na karshe da aka gan su kamar yadda dokoki na kasa da kasa suka tanada.
Wajibi ne Sojojin Najeriya su bayar da bayani a kan wadannan mutane da aka zalunta. Mutane nawa suka kashe kuma suka binne a boye a cikin kabari na bai-daya? Mutane nawa ne kuma har yanzu suke tsare da su a boye a wuraren tsare jama’a na sirri da ke fadin tarayyar Najeriya?
Harkar Musulunci a Najeriya tana kara jaddada bukatarta ta a gaggauta sakin dukkanin ‘yan uwa na IMN da ake tsare da su, wadanda suka hada da wadanda Sojoji suke tsare da su da kuma wadanda aka tsare a wuraren tsare jama’a da ke fadin kasar nan. Hakazalika kuma muna bukatar a ba mu dukkanin gawawwakin wadanda Sojoji suka kashe, wadanda suka hada har da wadanda suka binne a kokarinsu na boye mummunan laifin da suka aikata, domin a gan su, danginsu su tantance su domin su yi masu jana’iza irin yadda Addinin Musulunci ya tanada.
Daga karshe, muna nuna goyan bayanmu da kuma kasancewa tare da Amnesty International wajen raya wannan rana, da kuma yin kira ga Mahukunta na Najeriya da su fito fili su yi bayani kan wadanda aka tilasta bacewarsu tare da kuma gurfanar da wadanda ake tukuma da aikata wannan aika-aika a gaban shari’a domin samun adalci.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
Skype: Ibrahim musa42
31/08/2017


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky