Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Iran: Shugaba Hassan ya sami kuri'u miliyan 22,796,468

Sakamakon  Zaben Shugaban Kasar Iran: Shugaba Hassan ya sami kuri'u miliyan 22,796,468

Hukumar Zaben, da ta sanar da sakamakon ta ce; ya zuwa yanzu Shugaba Hassan Rauhani yana kan gaba da kuri'a Miliyan 14.

Hukumar Zaben, da ta sanar da sakamakon ta ce; ya zuwa yanzu Shugaba Hassan Rauhani yana kan gaba da kuri'a Miliyan ashirin da biyu, da dubu dari bakwai da cas'in da shida, da dari hudu da sittin takwas.

Tun da fari Shugaban hukumar zaben, Ali Asgar Ahamdi, da ya ke bayani a gaban manema labaru da safiyar yau, asabar,ya ce; An kirga kuri'u miliyan ashirin da biyar, da dubu dari da tamanin, da  biyu, da dari uku da goma, Hassan Rauhani ya sami kuri'u, miliyan goma sha hudu, da dubu dari shida da goma sha tara, da dari takwas da arba'in da takwas. ( 14,619,848 )

Sai kuma Sayyid Ibrahim Ra'isi, Sadat, wanda ya sami kuri'a miliyan goma, da dubu dari da ashirin da biyar, da dari takwas da hamsin da biyar. (  10,125,855). A yanzu, Ra'isin ya kara samun kuri'un da su ka kai miliyan 15.

Sai Mustafa Agha Mir Salim, wanda ya sami kuri'a dubu dari biyu da cas'in, da dari biyu da saba'in da shida.

Sai Mustafa Hashimi Taba, wanda ya sami kuri'u dubu dari da talatin da tara, da dari uku da talatin da daya.

Jumillar kuri'un da aka kada sun haura miliyan 40


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky