Rundunar ‘Yan sanda ta Jahar Kaduna ta baje kolin masu laifi

Rundunar ‘Yan sanda ta  Jahar Kaduna ta baje kolin masu laifi

> Rundunar ‘Yan sanda ta
> Jahar Kaduna ta baje kolin masu laifi


> Kwamishinan 'Yan Sanda
> na jihar Kaduna, Agyole Abeh ya
> gabatarwa da manema labarai wasu masu laifuka da suka hada
> da fashi da makami,
> satan shanu da kuma garkuwa da mutane dan neman kudin fansa
> domin nuna
> nasarorin da suka samu a yan kwanakin da suka gabata.
> 
> Daga cikin wadanda ake
> zargi da aikata laifukan, an kama
> wasu da miyagun makamai da suka hada da bindigogi kirar gida
> katukan ATM guda
> uku.
> 
> Kwamishinan ya sha
> alwashin daukan kwararan matakai don kawo
> karshen aikata manyan laifuka a jihar musamman a kan
> hanyoyin Abuja zuwa Kaduna
> da kuma na Binnin Gwari da suka yi kaurin suna.
> 
> A wata takardar sanarwa da
> suka ba manema labarai,
> kwamishinan ya yi kira ga iyayen yara da su ja kunnen
> ‘yayansu akan fadawa
> cikin miyagun laifuka da suka hada da sara-suka da sace-sace
> a unguwanni.  
> 
> Daga karshe kuma yayi kira
> ga jama’ da su ci gaba da taimaka
> musu da muhimman bayanai don samar da tsaro a
> jihan.

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky