Ruhani:Trump Zai Haifar Da Rikici Ne A Gabas Ta Tsakiya

Ruhani:Trump Zai Haifar Da Rikici Ne A Gabas Ta Tsakiya

Dakta Hasan Ruhani Shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran yayi kakkausar suka ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump na sanar da Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila yana mai cewa babu abin da hakan zai haifar in ban kirkiro wani sabon rikici a yankin Gabas ta tsakiya.

Dr Ruhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai jim kadan bayan tashinsa zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya don halartar taron shugabannin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da za a gudanar a yau din nan Laraba don tattauna wannan batu da shugaban Amurkan ya tayar da kuma matsayar da ya kamata kasashen musulmi su dauka kan hakan.

Shugaba Ruhani ya ce Qudus dai ta dukkanin musulmi ne sannan kuma ita ce babbar birnin kasar Palastinu, don haka matukar dai suka kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu, wannan matakin yana iya zama wata nasara ga musulmin da kuma yankin baki daya.

Shugaban na Iran ya kara da cewa: Sakon mu dai shi ne cewa lamarin Palastinu shi ne mafi girma da muhimmancin lamurran da suka shafi musulmi da kuma duniyar musulmi, don haka ya zama wajibi a yi Allah wadai da wannan matsaya ta Trump, yana mai sake jaddada matsayar Iran ta ci gaba da goyon bayan Palastinu da kuma Palastinawa har sai sun cimma burinsu na 'yanto kasarsu daga mamayar yahudawa 'yan share guri zauna.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky