Ruhani Wajen Bikin Ranar Sojoji: Iran Za Ta Mayar Da Martani Da Masu Wuce Gona Da Iri

Ruhani Wajen Bikin Ranar Sojoji: Iran Za Ta Mayar Da Martani Da Masu Wuce Gona Da Iri

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar dakarun sojin Iran ba barazana ba ce ga kasashen makwabta da kuma yankin Gabas ta tsakiya, to amma za su mayar da martani mai kaushin gaske ga duk wanda yayi kokarin wuce gona da iri a kan Iran.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi a safiyar yau wajen faretin sojin kasa na kasar Iran da aka gudanar don tunawa da ranar sojoji ta kasar Iran din inda ya ce: Sojojin Iran ba za su zama barazana ga wani ba. Suna iyakacin kokarinsu wajen gujewa rikici, to sai dai a koda yaushe suna cikin shiri wajen tinkarar duk wani makirci, don haka ne suke kara irin karfin da suke da shi a kowane lokaci.

Shugaba Ruhani ya kirayi kasashen da suke makwabtaka da Iran da su kwantar da hankalinsu don kuwa karfin da Iran take da shi, karfi ne na kariyar kai ba na wuce gona da iri a kan kowa ba.

Bikin na yau dai, baya ga shugaba Ruhanin, har ila yau ya sami halartar manyan hafsoshin sojojin kasa, sama da na ruwa bugu da kari kan manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran, inda sojojin suka nuna wasu daga cikin makaman da suke da su da wadanda aka kera su cikin shekarun baya-bayan nan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky