Rouhani: Iran Zatayi Nasara Akan Makiya

Rouhani: Iran Zatayi Nasara Akan Makiya

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar a halin yanzu Iran ba ta kiyayya da wata kasa in ban da Amurka, haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan amshin shatansu, don haka sai ya ce: Al'ummar Iran ta hanyar hadin kai da aiki tare za su yi nasara kan makiyansu.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi wajen taron tunawa da tsohon shugaban kasar ta Iran Shahid Ali Raja'i, inda yayin da yake magana kan cewa har abada al'ummar Iran ba za su mika wuya ga matsin lambar Amurka ba, ya bayyana cewar: Al'ummar Iran dai ba za ta taba mika kai ga wasu gungun mutane masu mulki a fadar White House ta Amurka wadanda su kansu ba su san me suke fadi da kuma abin da ya kamata su aikata ba.

Rouhani ya ci gaba da cewa: Wadannan sabbin masu mulkin Amurka, ba wai kawai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke fada ba, face ma dai har da  tsoffin abokansu da kuma ma kasashen da suke da alaka ta tattalin arziki mai girman gaske.

Shugaban na Iran yayi watsi da batun tattaunawa da Iran da Amurka take gabatarwa yana mai cewa babu yadda za a iya tattaunawa karkashin irin wannan matsin lamba da take yi wa al'ummar Iran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky