Rasha Ta Kirayi Jakadan "Isra'ila" A Kasar Saboda Harin Da "Isra'ilan' Ta Kai Siriya

Rasha Ta Kirayi Jakadan

Kasar Rasha ta kirayi jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar don neman karin bayani dangane da keta hurumin kasar Siriya da jiragen yakin haramtacciyar kasar suka yi da kuma kai hare-hare wasu bangarori na kasar.

Kafafen watsa labaran haramtacciyar kasar Isra'ilan sun ba da rahoton cewa a jiya Juma'a ce Ma'aikatar harkokin wajen Rashan ta kirayi jakadan Isra'ilan a Mosko Gary Koren  kwana guda bayan da ya mika takardun kama aikinsa ga shugaban kasar Rashan Vladimir Putin don neman karin bayani kan wannan harin.

A jiya Juma'a ce dai rundunar sojin Siriyan suka fitar da wata sanarwa inda suka ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka shigo kasar da kai hare-hare kan wasu sansanoni na soji, inda suka ce sun harbe jirgi guda da kuma samun guda da harsashi yayin wannan harin.

Firayi ministan HKI Benjamin Netanyahu dai ya tabbatar da kai hari cikin Siriyan yana mai cewa sun kai harin ne kan wani sansani na dakarun Hizbullah a kasar Siriyan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky