Fira ministan Rasha ya gargadi kasar Amurka kan sake kakaba takunkumi kan kasarsa da cewa: Kakaba takunkumin yana matsayin shelanta yakin kasuwanci ne a tsakanin kasashen biyu.
A jawabin da ya gabatar a Kamchatka na kasar Rasha a yau Juma'a: Fira ministan Rasha Dmitry Medvedev ya gargadi kasar Amurka da cewa: Sake kakaba wasu sabbin takunkumi kan kasarsa musamman dangane da zargin Rasha da hannu a aiwatar da kisan gilla kan tsohon jami'in leken asirinta a kasar Birtaniya lamari ne da ke matsayin shelanta yakin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.
Medvedev ya kara da cewa: Kakaba takunkumin Amurka kan harkokin bankin kasar Rasha ko kudaden kasar yana matsayin shelanta yaki ne kan Rasha lamarin da zai fuskanci maida martani a fuskar kasuwanci ko siyasa ko kuma duk wata kafa da zata cutar da kasar Amurka a matsayin maida da martani.