Ranar Qudus Ta Duniya a Iran Miliyoyin Al'umma Suka Fito

Ranar Qudus Ta Duniya  a Iran Miliyoyin Al'umma Suka Fito

Tun da safiyar yau ne miliyoyin al'ummar Iran, maza da mata suka fito kan titunan kusan dukkanin garuruwan kasar don amsa kiran marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma raya Ranar Kudus ta duniya don sake jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta.

Rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar musamman a birnin Tehran, babban birnin kasar ta Iran, sun bayyana dubun dubatan al'ummar birnin ne da suka hada da manyan jami'an gwamnati, jami'an sojoji da na 'yan sanda, manyan malamai da sauran al'umma ne suka fito don nuna goyon bayan su ga al'ummar Palastinu da kuma yin Allah wadai da yahudawan sahyoniya da masu goya musu baya musamman Amurka da 'yan amshin shatansu.

Masu zanga-zangar dai suna rera take da kuma rike da kwalaye da tutoci da suke nuna yin Allah wadai dinsu da haramtacciyar kasar Isra'ila, Amurka da wasu shugabannin kasashen larabawa da suke hada kai da su wajen cutar al'ummar Palastinu.

Kimanin shekaru 39 kenan marigayi Imam Khumaini ya  sanya ranar juma'ar karshe ta watan Ramalana a matsayin Ranar Kudus ta duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu yana mai kiran al'ummar musulmi da su girmama wannan ranar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky