Rana Ta Uku:Bukin Tunawa Da Munasabar Haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha a Kano

Rana Ta Uku:Bukin Tunawa Da Munasabar Haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha a Kano

Yau Asabar,5 ga watan Agusta 2017,ta zama ranar khatma na taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha da kuma sanya tuta a Hussainiyyar Kofar Waika Kano.
In ba a manta ba,wannan taro na Ad-Da’iral Ammah ce wanda Sheikh Zakzaky ya umurci Sheikh Sanusi AbdulKadir da ya shirya shi a garin Kano a wannan shekaran.Yau ce rana ta uku kuma ta karshe daga cikin kwanaki uku da aka dauka ana yin taron a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayyar Nigeriya.
Bayan bude taro da addu’a da wakokin bege daga sha’irai,malamai da dama sun yi jawabai masu yawa dangane da munasabar da aka taro domin ta.
Sarkin Sharifan Kano a nashi jawabin ya bayyana cewa:
“Duk wanda kuka ga ya shirya taron hadin kan musulmi amma bai gayyaci ‘yan shi’a ba,munafuki ne.Ba taron hadin kai bane,taron ya za a far wa ‘yan shi’a ne da neman biyan bukatunsu kawai.Ni Bakadire ne,kuma dan darika,na yarda ‘yan shi’a musulmai ne,kuma zan yi taro da su.
“Gidanmu ya kai shekara dari shida da sharifanci amma ban taba ganin tutar kabarin wani Imami ba,sai a gun ‘yan shi’a.”
Sarkin Sharifan Kano ya yi kira da roko ga Sheikh Sanusi AbdulKadir cewa ‘don Allah a taimaka a shiga da wannan tuta ta Imam Ridha cikin Sharifai a zagaya mana da ita a nuna masu cewa gashi wajen ‘yan shi’a.’
Sarkin Sharifai bai karkare jawabinsa ba sai da yayi kira ga hukuma yana cewa:
“Wannan taruka da ake yi na Imam Ridha sune suke zaunar da kasar nan lafiya.”
Shi kuwa Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako a wajen taron, yayi bayani ne game da muhimmancin riko da Imam Ali a matsayin wanda yake massala sunnar Annabi Muhummad(sawa),yana cewa:
“A lokacin da aka kawo Imam Ali wajen zaben khalifa na uku an bashi zabi akan in zai yi aiki da sunnar Annabi da sunnar khalifofi guda biyu,sai Imam Ali yace;zan yi aiki da Manzon Allah.Don haka idan kana neman sunnah,to,Imam Ali shine sunnah.”
Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa ‘Sheikh Zakzaky ya riga yayi jihadi kuma ya riga ya kafu.Ya ‘yantar da zukata,sun yi bara’a kuma sun yi wilaya,an canja tunaninsu.’
Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake jawabinsa a matsayin mai masaukin baki,ya bayyana cewa:
“Don girman Allah don matsayin Imam Ali Ar-Ridha don albarkan wannan tuta idan da wanda muka yi wa laifi,don girman wannan rana tuta ya yafe mana.
“Mu idan da wanda yayi mana laifi Wallahi mun yafe masa.Ranar sa wannan tuta ta zama ranar hadin kanmu.”
Taron ya samu halartan ‘yan uwa daga sassa daban daban a cikin Nigeriya a kasashen makwabta.Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro akwai Sheikh Adamu Tsoho Jos,Sheikh Kasimu Umar Sokoto,da Malam Abubakar Nuhu Talatan Mafara da sauran manya manya wakilan ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwa masu yawa

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky