Rahotanni: Mutanen Da Ake Zargi Da Kashe Khashoggi Na Da Alaka Da Cibiyoyin Tsaron Saudiyya

Rahotanni: Mutanen Da Ake Zargi Da Kashe Khashoggi Na Da Alaka Da Cibiyoyin Tsaron Saudiyya

A daidai lokacin da jami'an tsaron Turkiyya suke ci gaba da gudanar da bincike dangane da bacewar sanannen dan jaridar nan dan kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi, wasu rahotanni na nuni da cewa mutanen da ake zargi da hannu cikin mutuwar Khashoggin suna da alaka da cibiyoyin tsaro da kuma fadar mulkin Saudiyyan.

A wani rahoto da ta buga, jaridar Washington Post ta Amurka ta bayyana cewar mutane 12 daga cikin mutane 15 da ake zargi da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa dan jaridar, suna da alaka ta kut da kut da cibiyoyin tsaro da na leken asiri na Saudiyyan.

Jaridar ta ce ta samu hotunan fasfo na wadannan mutanen da ke nuni da cewa wasu daga cikinsu suna daga cikin jami'an tsaro na fadar mulkin Saudiyya. Har ila yau ta ce daya daga cikin mutanen yana daga cikin masu tsaron lafiyar Yarima mai jiran gado na Saudiyyan Muhammad bn Salman, kamar yadda wasu biyu daga cikinsu kuma suna aiki ne a ofishin Ibn Salman din.

Jami'an tsaron kasar Turkiyya din dai suna ci gaba da gudanar da bincike kan batun bacewar dan jaridar Jamal Khashoggi tun bayan da ya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul na kasar Turkiyya don karbo wasu takardu. Bayanai dai suna nuni da cewa jami'an tsaron Saudiyyan da suka zo karamin ofishin jakadancin sun kashe dan jaridar ne sakamakon sukar siyasar Saudiyyan da yake yi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky