Palastinawa Biyu Sunyi Shahada A Yankin Gaza

Palastinawa Biyu Sunyi Shahada A Yankin Gaza

Ma'aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa Palasdinawa biyu ne sukayi shahada a wani hari da sojojin H.K. Isra'ila suka kai da safiyar yau Lahadi.

Kungiyar Hamas ta ce matasan biyu sun yi shahada  ne sakamakon harin tankar yakin sojojin yahudawa 'yan kama wuri zauna suka kai masu, a gabashin birnin Rafa.

Matasan biyu sun hada da Hussein al-Amour, dan shekara 25 da kuma Abdel Halim al-Naqa, mai shekara 28.

Wasu alkalumma da ma'aikatar lafiya ta yankin Gaza ta fitar sun nuna cewa Palasdinawa 118 ne suka yi shahada sakamakon harbin sojojin Isra'ila tun bayan kaddamar da zanga zanga da Palasdinawa ke yi na kwato hakkokinsu a ranar 30 ga watan Maris da ya gabata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky