Nijeriya : Za'a Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargin Alaka Da Boko Haram

Nijeriya : Za'a Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargin Alaka Da Boko Haram

Rahotanni daga Nijeriya na cewa yau Litini za'a fara gurfanar da mutanen da ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram.

Majiyoyin shari'a sun ce za' a gurfanar da kashin farko na masu zargin kimanin dubu da dari shida cikin makwanni masu zuwa a wasu cibiyoyin tsare mutane a kasar, daga bisani kuma sauren su kimanin 5,000 a yi musu nasu shari'o'in, kuma ko wanne za'a gurfanar da shi, shi kadai muddun dai laifinsa bai da alaka da wani.

Wannan dai shi ne karon farko da za' a yi wa mutane da suka kai irin wannan adadi shari'a kan zargin alaka da kungiyar Boko Haram.

Hukumomi shari'a a kasar sun ce za' a yi zaman shari'o'i ne a cibiyoyin tsare mutanen da ke sassan kasar, maimakon a kotuna.

Kafin hakan dai kungiyoyin kare hakkin dan adam a wannan kasa ta Nijeriya sun dade suna sukar jami’an tsaron kasar da kame fararen hula da sunan ‘yan Boko Haram ba tare da an gurfanar da su a kotu ba..288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky