Nijeriya : Osinbajo, Ya Gana Da Buhari A Landan

Nijeriya : Osinbajo, Ya Gana Da Buhari A Landan

Mataimakin shugaban tarayya Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaba Mahammadu Buhari da ke jinya a birnin Landan na kasar Biritaniya.

Wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter, a jiya Talata ta ce bangarorin biyu sunyi kyakyawar ganawa, kuma a nan gaba za'a yi wa jama'a karin bayyani kan yadda tattaunawar shugabannin biyu ta kasance.

Shugaba Muhammdu Buhari na Najeriya dai ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a Landan ba tare da an bayyanawa al'umma hakikanin rashin lafiyar da ke damunsa ba ya gana da mataimakinsa a jiya a karon farko.

Kafin hakan dai gwamnatin kasar ta jima tana musunta cewa shugaban kasar mai shekaru 74 na cikin mayuyacin hali kamar yadda wasun 'yan kasar ke nanatawa.

A ranar bakwai ga watan Mayu da ya gabata ne dai shugaba Buhari, ya sake komawa Birtaniya domin jinya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky