Nigeria: 'An kashe 'yan Shi'a hudu' a Kano

Nigeria: 'An kashe 'yan Shi'a hudu' a Kano

Kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta mabiya Shi'a a Najeriya (IMN) ta ce an kashe akalla mambobinta "hudu", yayin da 'yan sanda suka tarwatsa wani tattaki da 'yan kungiyar suke yi a Kano ranar Lahadi.

Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya ce suna tattakin Arbaeen ne yayin da al'amarin ya faru a kan hanyarsu ta zuwa garin Zaria daga Kano.

Ya ce cikin mutanen da suka rasa rayukansu har da mata biyu. Kuma kakafin kungiyar ya ce akwai wadanda suka jikkata da dama.

Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Kano DSP Magaji Musa ya tabbatar wa BBC cewa jami'ansu sun tarwatsa tattakin "ba tare da nuna karfin tuwo ba, saboda taron ya saba wa doka."

Mun gargadi shugabanninsu kan kada su fito wannan tattakin," kamar yadda ya ce.

'Yan kungiyar suna tattakin ne don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW) Imam Hussain ya shiga.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky