Najeriya: Boko Haram Ta Kwace Iko Da Garin Gulak A Jahar Adamawa

Najeriya: Boko Haram Ta Kwace Iko Da Garin Gulak A Jahar Adamawa

Jaridar Daily Trust ta ce; Daruruwan Mazauna Garin Na Gulak Da Ke Karamar Hukumar Madagali na jihar Adamawa, Sun Gudu Zuwa Daji domin tsira da rayukansu

Jaridar ta ambato wani mazaunin garin da ya gudu zuwa cikin daji yana cewa suna jin karar harbe-harben bindigogi daga inda suke.

Maharan sun ci karfin sojoji da kuma 'yan sanda da su ke a garin na Gulak da suka kwace iko da shi.

A wani labarin na daban, da  Kamfanin dillancin labarun Fransa ya ambato majiyar gwamnati, ya ce "Yan Boko haram su 20 sun kai hari a garin Jaddannam inda suka kashe mutane 6.

Jami'in gwamnati a garin na Jaddannam mai suna Bukar Wakil Tawu ya ce; Baya ga asarar rayuka da harin na Boko haram y ahaddasa, ya kuma yi sanadin asarar dukiyar mutanen yanki mai yawa.

A cikin watan Yuni na wannan shekarar ma, yan kungiyar ta Boko haram sun kai wani hari a yankin wanda ya yi sanadin mutuwar masu binciken man fetur su 70.

Tun shekarar 2009 ne dai Najeriya take fama da matsalar boko haram, wanda zuwa yanzu ya ci rayuka masu yawa. Kasashen da suke makwabtaka da Najeriya, da suka hada Nijar da Kamaru da Chadi ma suna fama da matsalar tsaro sanadiyyar kungiyar ta boko haram.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky