Najeriya: An kama Wani kwamandan Boko Haram

 Najeriya: An kama Wani kwamandan Boko Haram

sojojin Najeriya a Jihar Borno sun sanar da hallaka wasu mayakan kungiyar Boko haram 5 tare da kame Kwamandansu yayin wani sumame da suka gudanar a maboyar mayakan da ke dajin Sambisa a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mataimakin babban daraktan rundunar Operation Lafiya Dole kanal Onyeama Nwachukwu, ya ce dakarun sun kuma kubutar da wasu fararen hula 3 da ke rike a hannun mayakan tare da kame wasu tarin makamai da kuma ababen hawa.

A cewar Nwachukwu yayin samamen da aka shafe kwanaki biyu ana yi an kuma raunata dakarun sojin Najeriyar 3 yayinda yanzu haka su ke ci gaba da karbar kulawar agggawa.

A cewar Nwachukwu sumamen, yunkuri ne na kakkabe sauran mayakan kungiyar ta Boko Haram da ke ci gaba da kai hare-haren sari-ka-noke, tare kuma da kubutar da fararen hular da suke ci gaba da garkuwa da su.

Nwachukwu ya ce a ranar juma’a ne aka kaddamar da sumamen mai taken ‘‘CAMP ZAIRO’’ mai nufin lalubo sauran maboyar mayakan.

Acewarsa har yanzu dai ana ci gaba da sumamen don tabbatar da kubutar da sauran fararen hular da ke hannun ‘yan ta’addan tare da murkushe su a bangare guda ciki kuwa har da hare-hare ta sama da ake ci gaba da kai wa.

Sumamen rundunar ta Operation LAFIYA DOLE na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da zaman zullumin bacewar ‘yan matan sakandiren Dapchi a jihar Yobe da ake zargin mayakan na Boko Haram da sacewa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky