Najeriya: An Gudanar Da Zanga-zangar Neman A Saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Najeriya: An Gudanar Da Zanga-zangar Neman A Saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Daruruwan mutane ne suka yi Zanga-zangar a birnin Abuja, suna masu kira da saki jagoran harkar musulunci domin ya nemi magani

Bugu da kari a jiya a birnin Abujan, wasu kungiyoyin farar hula sun fara zaman dirshan na neman ganin an saki shehun malamin.

A cikin kwanakin bayan nan, mambobin harkar musulunci a karkashin jagorancin Shekih Ibrahim Yakubu El-Zakzaky sun gudanar da jerin gwano a yankunan arewacin kasar daban-daban da suka hada da Abuja, bisa labarin tabarbarewar lafiyarsa.

Tun a ranar 13 ga watan Disamba na 2015 ne dai ake saro da shi, bayan da sojoji suka afkawa gidansa da ke birnin Zaria a jahar Kaduna.

Daruruwan mutane ne dai sojojin kasar suka kashe daga cikin hadda 'ya'yan Sheikh Zakzaky guda uku.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky