Nageria: Kimanin 'Yan Shi'a Goma Ne Sojojin Kasar Suka Kashe

Nageria: Kimanin 'Yan Shi'a Goma Ne Sojojin Kasar Suka Kashe

Kakakin harkar Islamiyya a Najeriya Malam Ibrahim Musa ne ya sanar da cewa an kashe mutane 10 din a kusa da babban birnin kasar Abuja

Sojojin Sun bude wuta ne ba tare da wani gargadi daga mahukunta kasar ba dangane da tattakin na arba'in.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da jami'an tsaron Najeriya suke bude wuta akan Masu juyayin Ashura da kuma tattakin arba'in na Ashura. A ranar 13 ga watan Disamba na 2015 sojojin kasar sun kai hari akan Husainiyar Bakiyatullah da ke birnin Zaria a jahar kaduna da ke arewacin kasar. Daruruwan mutane ne sojojin su ka kashe a yayin wancan harin.

Jagoran harkar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky yana a tsare fiye da shekaru uku da su ka gabata. Sojoji sun kashe uku daga cikin 'ya'yansa a yayin farmakin da su ka kai a birnin Zaria.

A shekarar 2016 wata kotu a kasar ta yanke hukunci da a saki shehun malamin, sai dai har yanzu mahukuntan kasar ba su aiwatar ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky