Myanmar za ta mayar da 'yan kabilar Rohingya muhallansu

Myanmar za ta mayar da 'yan kabilar Rohingya muhallansu

Gwamnatin Myanmar ta ce ‘yan gudun hijirar musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke shirin komawa jihar Rakhine ba za su dawwama a sansanin ‘yan gudun hijira ba, face sai ta tabbatar da kowannensu ya koma muhallinsa na asali.

Mynamar dai ta samar da guraben da za ta sauki daruruwan ‘yan kabilar ta Rohingya da ke gudun hijira a Bangladesh amma kawo yanzu babu ko da mutum guda cikin fiye da mutane dubu dari 7 da ya koma jihar tun bayan kisan kiyashin da jami’an tsaron kasar suka rika yi musu bayan wani rikici tsakaninsu da mabiya addinin Budda a kasar mai karancin musulmi.

Majalisar dinkin Duniya ta ce matukar da gaske Mynamar din na bukatar komawar daruruwan ‘yan kabilar ta Rohingya dole ne ta dauki matakan kare rayukansu.

A bangare guda suma daruruwan ‘yan gudun hijirar da ke zaune a bangaladesh karkashin wata kungiya guda da suka kafa sun bukaci lallai Myanmar ta cika musu wasu sharudda da suka gindaya kafin amincewa da komawarsu jihar Rakhine.

Daga cikin sharuddana da suka gindaya akwai sakar musu mutanensu da gwamnatin ke rike da su a gidajen yari, sai kuma batun tabbatar da su a matsayin cikakkun ‘yan kasa baya ga alkawarin kare rayukansu.

Ko a baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin na Myanmar a matsayin yunkurin shafe wata kabila, matakin da ya sa ta bukaci shugabar gwamnatin ta Myanmar Aung San Suu Kyi yi mata bayani kan matakan da take dauka don kare rayukan 'yan kabilar ta Rihingya amma ta gaza cewa uffan


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky