Mutane Fiye Da Miliyan Uku Ne Ake Sa-Ran Zasu Gudanar Da Juyayin Ashura A Karbala

Mutane Fiye Da Miliyan Uku Ne Ake Sa-Ran Zasu Gudanar Da Juyayin Ashura A Karbala

Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa: Ana sa-ran yawan jama'ar da zasu halacci zaman makokin ranar Ashura a birnin Karbala na kasar zasu haura mutane miliyan uku daga ciki da wajen kasar.

Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa: Ana ci gaba da samun tururruwan jama'a da suke zuwa birnin Karbala domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar goma ga watan Muharram lamarin da ke nuni da cewa; Akwai yiyuwar yawan jama'ar da zasu halacci juyayin a bana zai haura mutane miliyan uku.

Jamal Shahristani shugaban bangaren sanarwa a cibiyar kula da masu ziyarar wajaje masu tsarki a kasar Iraki a jiya Asabar ya bayyana cewa: A halin yanzu haka birnin Karbala tana ci gaba da karbar baki daga ciki da wajen kasar da suka zo domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar 10 ga watan Muharram, don haka ake hasashen yawan jama'ar da zasu halacci juyayin na bana zai haura mutane miliyan uku, inda ko a shekararda ta gabata fiye da mutane miliyan biyu ne suka gudanar da juyayin.

A yau Lahadi ne dai za a gudanar da zaman taron juyayin Ashura a birnin Karbala na kasar Iraki domin jaddada alhini da juyayi kan gisan gillar da Bani-Umayyah da magoya bayansu suka yi wa jikan manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna Imam Husani dan Ali dan Abi-Talib {a.s} da iyalan gidansa da sahabbansa da ba su wuce 72 ba, a filin Karbala na kasar Iraki a shekara ta 61 bayan hijira, bayan sun bijirewa mulkin kama karya da bakin zalunci na mahukuntan Bani-Umayyah karkashin ja'irin shugaba Yazid dan Mu'awiya da dukkanin Musulmi suka yi tarayya kan fasikancinsa da rashin cancantarsa ga jagorancin al'ummar musulmi. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky