Mutane Biyu Sun Rasa Rayukan Su Yayin Zanga-Zangar Kiran A Saki Sheikh Zakzaky A Kaduna

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukan Su  Yayin Zanga-Zangar Kiran A Saki Sheikh Zakzaky A Kaduna


Rahotanni daga Nijeriya sun tabbatar da cewar mutum biyu sun rasu wasu kuma sun sami raunuka a lokacin da 'yan sanda suka fada wa 'yan kungiyar Harkar Musulunci ta kasar da suka fito don gudanar da zanga-zangar a saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnatin Nijeriya ta ke ci gaba da tsare shi sama da shekaru biyun da suka gabata.

Rahotannin sun ce wannan lamarin dai ya faru ne a jiya Lahadi lokacin da mabiyar Sheikh Ibrahim Zakzaky din suka fito a garin Kaduna don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsare malamin da gwamnati take yi da kuma kiran da a sake shi, inda jami'an tsaron kasar suka fada musu da nufin tarwatsa su, lamarin da yayi sanadiyyar rasuwar mutum biyu sakamakon harbin da 'yan sandan suka yi masu.

Baya ga garin na Kaduna dai, har ila yau an gudanar da irin wadannan zanga-zangogi a wasu garuruwa masu yawa na Nijeriya din.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan wasu labarai ne da suke nuna cewa, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya din Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, da suka hada da yiyuwar shanyewar jikinsa, a inda ake tsare shi, da yake bukatar kula ta likitoci na gaggawa. Don haka masu zanga-zangar suka kira gwamnatin Muhammadu Buhari ta kasar da ta gaggauta sako shi don fita da shi wajen kasar don sama masa kula ta musamman cikin gaggawa


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky