Mutane 4 Daga Cikin wadanda Ake Zargi Kan Kisan Alkali Sun Mika Kansu

Mutane 4 Daga Cikin wadanda Ake Zargi Kan Kisan Alkali Sun Mika Kansu

Mutane 4 daga ciki har da hakimin Dura-Du na karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau ta tarayyar Najeriya sun mika kansu ga yansanda a jiya jumma'a bayan da yansanda suka sanya sunayensu a cikin wadanda ake nema.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto majiyar Jami'an 'yansanda a jihar Plateau tana cewa Yakubu Rapp hakimin Dura-Du na karamar hukumar Jos ta Kudu, da kuma wasu mutane 3 daga cikin wadanda yansandan suke nema sun mika kansu ga yansanda a jiya Jumma'a.

Tema Tyopev, kakakin yan sanda a jihar Plateau ya ce mutanen 8 ne yansandan suke nema don amsa tambayoyi kan bacewar Manjo. Janar Alkali mai ritaya a cikin watan satumban da ya gabata a yankin nasu. Sauran mutane ukku da suka mika kansu sun hada da Timothy Chuwang, Mathew Chuwang da kuma Stephen Chuwang. 

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa wannan ya nuna cewa matakin 'yansandan suka dauka na sanya sunayen mutane 8 cikin wadanda ake nema ya yi amfani. 

Tema, ya kara da cewa a halin yanzu an fara yi masu tamboyoyi dangane da gaskiyan abinda ya faru da Manjo. Janar Alkali.

Kafin haka dai jami'an tsaro a jihar ta Plateau sun gano motar Alkali a cikin wani kududdufi a yankin Dura Du, sannan sun gano kabarinsa na farko kafin a kai shi wani wurin da har yanzun ba'a gane ba


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky