Mutane 30 Ne Su Kai Shahada A Harin Masallacin Herat Afganistan

Mutane 30 Ne Su Kai Shahada A Harin Masallacin Herat Afganistan

Wata majiya da ga Asibitin garin tace kimanin mutane 30 ne su kai shahada a sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai a Masallacin ‘yan Shi’a na garin Herat dake Afganistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-kafafen yada labarai na cikin gidan Afganistan  sun sanar da cewa sakamakon harin kunar bakin wake a kusa da masallacin ‘yan shi’a a garin Herat kimanin mutane 30 ne suka yi shahada inda wasu  8 suka samu munanan raunuka,

Majiyar daga asibitin ta sanar cewa, mutanen sunyi shahada ne a lokacin da wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da Masallacin yayin da mutane suke cikin sallah.

Mai Magana da yawun ‘yan sanda na garin Abdullah Walidzade yace: ga dukkan alamu maharan sun fi mutun daya.

Ya zuwa yanzu ba wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

An kai wannan harin ne kusa da masallacin jawadiya a garin Herat.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky