Ministocin Harkokin Wajen Rasha, Iran, Syria, Sun Gudanar Da Zama Yau A Moscow

Ministocin Harkokin Wajen Rasha, Iran, Syria, Sun Gudanar Da Zama Yau A Moscow

Ministocin harkokin wajen kasashen rasha, Iran da kuma Syria, sun gudanar da wani zama na musammana yau a birnin Moscow, domin tattauna muhimman lamurra da suka shafi halin da ake cikia Syria, da kuma daukar matakai na hadin gwiwa a tsakaninsu domin tunkarar lamarin.

Bayan kammala zaman da suka gudanar a yau a Moscow, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, da takwaransa na Iran Muhammad Jawad zarif, da kuma takwaransu na Syria Walid Mu'allim, sun gudanar da taron manema labarai na bai daya.

Dukkanin bangarorin sun nuna rashin amincewarsu da matakin da Amurka ta dauka na kai wa Syria hari ba tare da wata hujja a kan zargin da take yi a kan gwamnatin Syria ba.

Dukkanin bangarorin sun jaddada wajabcin kafa kwamiti mai zaman kansa da zai gudanar da bincike a kan hakikanin abin da ya faru, duk kuwa da cewa Amurka tana ta kokarin gujewa kafa kwamiti mai zaman kansa domin gudanar da wanann aiki.

Ministan harkokin wajen Rasha ya ce hukumar hana yaduwar makamai masu guba ta kafa wani kwamiti a halin yanzu domin gudanar da wannan aiki, amma akwai shakku dangane da kwamitin, domin dukkanin wadanda suke cikin kwamitin 'yan kasar Birtaniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky