Ministan Leken Asirin Kasar Iran Ya Sanar Da Kame Gungun 'Yan Ta'adda A Cikin Kasar

Ministan Leken Asirin Kasar Iran Ya Sanar Da Kame Gungun 'Yan Ta'adda A Cikin Kasar

Ministan leken asirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa: Jami'an tsaron Iran sun yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda a yankuna daban daban na kasar ta Iran a cikin 'yan kwanakin nan.

Ministan leken asirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Mahmud Alawi ya fitar da sanarwar cewa: Jami'an tsaron Iran sun gudanar da samame tare da samun nasarar cafke wasu gungun 'yan ta'adda a yankunan da suke yamma da kuma kudu maso yammacin kasar Iran a cikin 'yan kwanakin nan.

Har ila yau jami'an tsaron kasar ta Iran sun gano tarin makamai da bama-bamai da gungun 'yan ta'addan suke dauke da su, kuma bayan kammala gudanar da bincike kansu za a sanar da al'umma manufa da kuma aniyar 'yan ta'addan.

Sayyid Mahmud Alawi ya kuma bayyana cewa: Jami'an tsaron Iran sun gudanar da duk wasu shirye-shiryen da suka dace a fagen tsaro domin ganin an gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a ranar Juma'a mai zuwa a dukkanin fadin kasar Iran cikin kwanciyar hankali da aminci.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky