Miliyoyin Iraniyawa Sun sake fitowa A Yau Ma Don yin Allah Wadai Da Makiya Iran

Miliyoyin Iraniyawa Sun sake fitowa A Yau Ma Don yin Allah Wadai Da Makiya Iran

Miliyoyin Iraniyawa a garuruwa da kuma birane da dama sun fito kwanaki biyu a jere suna nuna goyon bayansu ga tsarin musuluncin da yake gudanar da kasar da kuma goyon baya ga jagorancin tsarin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto labarin cewa miliyoyin Iraniyawa a biranen Mashhad, Isfahan, Shiraz, Rasht, Yasoij, Ardabil da kuma Urumia, duk sun fito kan tituna suna Allah wadai da fitinar baya bayan nan da kasashen Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra'ila suke rurutawa a wasu wurare a cikin kasar.

Masu zanga-zangar suna dauke da manya-manyan hotunan jagoran juyin juya halin musulunci da kuma tutar kasar, har'ila yau suna dauke da hotunan shugaban kasar Amurka dauke da alamun ki da kuma Allah wadai a kansu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky