MDD Ta Yi Kira Da A Taimakawa "Yan Gudun Hijirar Daga Boko Haram

MDD Ta Yi Kira Da A Taimakawa

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD tana cewa; Da akwai bukatar dalar Amurka miliyan 160 saboda yan gudun hijirar boko haram

Hukumar ta ci gaba da cewa; Da akwai mutane dubu 208 daga Najeriya da wasu 75,000 a Nijar da Kamaru da Chadi, suna da bukatar taimako.

Wani sashe na bayanin MDD ya ce; 'Yan gudun hijirar suna rayuwa ne a cikin yankunan da su ma su ke fama da talauci a cikin kasashen da suka karbin bakuncinsu.

A shekarar 2017 hukumar 'yan gudun hijirar MDD ta bukaci kudaden da suka kai dalar Amurka miliyan 2041, amma ta iya samun kaso 56% kawai.

FIye da mutane dubu 20 ne Boko haram ta kashe a cikin Najeriya, Nijar, Chad, da Kamaru daga 2009 zuwa yanzu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky