MDD Ta Fitar Da Kudiri Kan Tsagaita Wuta A Syria

MDD Ta Fitar Da Kudiri Kan Tsagaita Wuta A Syria

A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya, ya fitar da kudiri kan tsagaita wuta a wuraren da aka killace 'yan ta'adda a Syria musamman yankin Gouta da ke gabashin birnin Damascus tsawon wata guda.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, dukkanin mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ne suka amince da kudirin, bayan kwashe tsawon kwanaki ana tafka muhawara a kansa.

Tsawon makonnin da suka gabata, 'yan ta'addan Jabhat Nusra da ke samun goyon baya da dauki daga kasashen Amurka, Saudiyya da kuma Isra'ila, da suka kafa sansaninsu a yankin Gouta da ke gabashin birnin Damascus, sun ta harba daruruwan makaman roka a kan birnin na Damascus, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, wanda hakan yasa ala tilas dakarun na Syria daukar matakan murkushe 'yan ta'addan.

Jakadan Syria a majalisar dinkin duniya Bashar Jaafari ya bayyana cewa, gwamnatin Syria za ta mutunta wannan kudiri, amma hakan ba zai shafi 'yan ta'addan ISIS, da Jabhat Nusra ba, inda ya ce gwamnatin Syria ba zata taba dakatar da yaki da wadannan kungiyoyin ba har sai an murkushe su.

Dubban 'yan ta'adda ne masu dauke da akidar wahabiyanci daga kasashen duniya suke yaki da gwamnatin Syria, wadanda suke samun dauki daga gwamnatocin Amurka, Saudiyya da kuma Isra'ila da Turkiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky