MDD : Kisan Kiyashi Ne Akewa Musulmin Rohingyas

MDD : Kisan Kiyashi Ne Akewa Musulmin Rohingyas

Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta kalubalanci abunda ta kira misali na kisan kiyashi dake faruwa a kasar Myammar.

Da yake bayyana hakan a gun bude taron hukumar karo na 36 yau Litini a birnin Geneva, Babban kwamishinan hukumar, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce abunda ke faruwa kan tsirarun musulmi 'yan Rohingyas a Myammar misali ne na kisan kiyashi.

Jami'in ya ce duk yunkurin hukumar na ganin tawagarta ta samu isa yankin domin ganin hakikanin abunda yake faruwa ya cutura.

Hukumar ta ce ta aike da wata tawagar masu bincike a kasar ta Myammar saidai bata samu izini shiga yankin da lamarin ke faruwa ba daga hukumomin kasar ta Myammar, amman tabas a cewar jami'in abunda ke faruwa misali ne na kisan kiyashi da ake 'yan kabilar ta Rohingyas.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky