MDD: Boko Haram Sun Sace Sama Da Kanana Yara 1000, Tun Daga 2013

MDD: Boko Haram Sun Sace Sama Da Kanana Yara 1000, Tun Daga 2013

Hukumar Kula Da Kananan Yara Ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta sanar da cewa 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram sun sace sama da kananan yara 1000 a yankunan arewa maso gabashin Nijeriya tun daga shekara ta 2013.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugaban hukumar ta UNICEF a Nijeriya, Mohamed Malick Fall ne ya sanar da hakan inda yace kananan yara a yankunan arewa maso gabashin Nijeriyan suna ci gaba da fuskantar barazana daga wajen 'yan kungiyar, inda yace hukumar tasa ta sami tabbaci cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun sace samar da yara 1000 wanda akwai yiyuwar adadin ya dara haka sosai ma.

Har ila yau Hukumar ta ce ya zuwa yanzu sama da malaman makarantu 2,295 ne aka kashe, sannan wasu makaratun kuma sama da 1,400 aka lalata su sakamakon wannan rikici na Boko Haram.

Kusan shekaru goma kenan 'yan kungiyar Boko Haram din suka kaddamar da hare-haren ta'addanci a Nijeriya wanda ya zuwa yanzu wasu dubban 'yan kasar ne suka rasa rayukansu baya ga wasu miliyoyi da suke sansanonin 'yan gudun hijira sakamakon wannan rikicin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky