Mauludin Sayyidah Fatimah [AS] na 'yan uwa mata a Kano ya isar da sako

Mauludin Sayyidah Fatimah [AS] na 'yan uwa mata a Kano ya isar da sako

Gagarumin bukin maulidin Sayyidah Fatimah Azzahra[AS] da aka gabatar a bana a Kano na shekara shekara da 'yan nuwa mata suka saba gabatarwa a ko wacce shekara a watan Jimada Thani daidai da ranar tunawa da haihuwar Sayyidatu Nisa'il Alameen ya aika da sako a tsakanin al'ummar musulmi..

Shi dai wanna bukin na bana an gabatar da shi ne a wannan Asabar din data gabata a babban dakin taro na hotel din ROYAL TROPICANA dake cikin birnin na Kano. 

Bayan an kammalabangaren farko na taron an tafi yin sallah da cin abinci da nufin daga nan za'a dawo dakin taro don kamala sauran abin da ya rage, kwatsam sai ga jami'an tsaro sun shigo suna tada jijiyar wuya suna cewa lallai sai a dakatar da taron kamar yadda aka basu umurni daga Abuja.

Dr Sunusi Abdulkadir ya gabatar da jawabin rufewa aka salami mahalarta.

Sai dai tare da irin wannan matsala da jami'an tsaron suka kawo a bana bukin ya aika da sako a ciki da wajen garin na Kano.

Ranar haihuwar Sayyidah Fatimah [AS] ita ce ranar mata ta duniya wadda ake daukan seerar rayuwar ta a matsayin abin koyi ga daukakin al'ummar mata na duniya.

Don haka a bana ma an gabatar da abubuwan koyi daban daban da suka hada da rayuwar aure a addinin musulunci, tabiyyar 'ya'ya, fuskantar munanan al'adu da dai sauran su.

Manema labarai daga tasoshin talbijin na AIT, Channels Tel, da sauran kafafen yada labarai duk sun halarci wannan buki na bana a Kano.

Alhamdullah wannan sako ya isa ga daukakin al'umma


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky