Masar Ta Bayyana Damuwarta Kan Dawowar 'Yan Kungiyar Da'ish Zuwa Yankin Arewacin Afrika

Masar Ta Bayyana Damuwarta Kan Dawowar 'Yan Kungiyar Da'ish Zuwa Yankin Arewacin Afrika

Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana tsananin damuwarsa kasarsa kan yiyuwar dawowar 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish zuwa yankin arewacin Afrika bayan kashin da suka sha a kasashen Siriya da Iraki.

A ganawarsa da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya Ghassan Salameh a birnin Alkahira a jiya Lahadi: Ministan harkokin wajen kasar Masar Samaha Shukri ya bayyana damuwarsa kan yadda ayyukan ta'addanci suke kara yawaita a duniya tare da nuna fargabarsa kan yiyuwar dawowar 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish zuwa yankin kasashen arewacin Afrika musamman kasar Libiya bayan kashin da suka sha a kasashen Siriya da Iraki lamarin da ke matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

Samaha Shukri ya kara da cewa: Gwamnatin Masar da dukkanin kasashen da suke makobtaka da kasar Libiya suna goyon bayan siyasar Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Libiya tare da jaddada bukatar ci gaba da kokarin warware rikicin kasar ta Libiya ta hanyar lumana.

A nashi bangaren wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kasar Libiya Ghassan Salameh ya fayyace irin matakan da suka cimma da kungiyoyin kasar Libiya da shirye-shiryensu kan makomar kasar a nan gaba musamman shirin gudanar da zabuka a kasar ta Libiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky