Martanin gwamnatin Tarayya ga 'Amnesty International' abin tsoro ne....

Martanin gwamnatin Tarayya ga 'Amnesty International' abin tsoro ne....

Hankalin Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ya koma ga wani martani mai shafi hudu da Ma'aikatar Harkokin kasashen waje, Abuja ta yi dangane da rahoton shekara-shekara na kungiyar Amnesty International na 2015/2016. Martanin da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma'aikatar, mai dauke da kwanan watan 03/03/2017, lallai akwai kurakurai masu yawan gaske a cikin sa..

Hankalin Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ya koma ga wani martani mai shafi hudu da Ma'aikatar Harkokin kasashen waje, Abuja ta yi dangane da rahoton shekara-shekara na kungiyar Amnesty International na 2015/2016. Martanin da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma'aikatar, mai dauke da kwanan watan 03/03/2017, lallai akwai kurakurai masu yawan gaske a cikin sa.

Abun da yafi jan hankalinmu shi ne abin da Ma'aikatar ta ce a shafi na biyu, sakin layi na biyar dangane da shari'ar Shaikh Ibraheem Zakzaky. Ma’aikatar ta bayyana cewa al'amarin Shaikh Zakzaky abu ne "mai matukar barazana ga tsaron kasa." Sannan ta ci gaba da zargin cewa ayyukan IMN baki daya, musamman Harkar da Shaikh Zakzaky ke jagoranta "ya yi kama da na Boko Haram, wanda kuma ya zama gagarumar matsala ba wai ga Najeriya kadai ba, har ma ga yankin tafkin Chadi da kuma duniya baki daya." Wannan wani zargi ne na shirme kuma marar tushe da Ma'aikatar ta yi.

Bari da farko mu yi nazarin wadannan batutuwan. Ana tsare da Shaikh Ibraheem Zakzaky tun Disambar 2015 bayan da sojojin gwamnatin Tarayya suka kai mamaya gidansa cikin dare ba tare da sahihiyar takardar umarni ba suka yi masa harbin kisa, tare da matar sa, ’ya’yan sa da kuma na kusa da shi, inda suka kashe ’yan kasa fiye da dubu wadanda ba su dauke da makami. Ta ya kuma za'a fassara wannan a matsayin "babban sha'anin tsaron kasa wanda ya yi kama da ayyukan Boko Haram"? Wannan magana da Ma'aikatar ta yi lallai babu shi da wata hujja sam kowace iri. Ba a taba samun Shaikh Zakzaky da kuma Harkar Musulunci da wani abu da ya danganci ta’addanci ba. Ba su taba daukan makami a kan wani ko gwamnatin Najeriya ba. Wannan kam hujja ne idan aka yi la'akari da irin tsananin muzgunuwa da ake nuna musu a watanni 15 da suka gabata. Idan har gwamnatin na da wani abu na tuhuma a kan Shaikh, me ya sa ba a kai shi kotu ba? Abin lura ne cewa, babu wata kotu a fadin Najeriya ko kuma ko'ina a duniya da ta taba samun Shaikh Zakzaky ko Harkar Musulunci da ayyukan ta'addanci. To, kuma yanzu daga ina aka samo wannan karyar na cewa wai ayyukan mu irin na Boko Haram ne?

Ma'aikatar ta ci gaba da cewa, "Abubuwan da Harkar El-Zakzaky ke yi babu gwamnatin dimokradiyya mai neman kawo ci gaba da za ta yarda da shi." Menene na ci gaba, kuma ina dimokradiyya a gwamnatin da ke take hakkin 'yan kasa da gangan? Ina dimokradiyya a gwamnatin da ke kin bin kundin tsarin mulkin kasa da dokokin kasa? Kar mu manta cewa gwamnatin Tarayya a hukumance ta sanar da babbar kotun kasa cewa Shaikh bai aikata laifin komai ba, wai ana ba shi "tsaron kariya" ne, wanda kotun ta bayyana a matsayin ya saba wa doka, ta kuma yi umarnin a sake shi, a biya shi diyya. Har yanzu ba su bi umarnin kotun kasa ba, duk da cewa suna kiran kan su a matsayin gwamnatin "dimokradiyya mai kawo ci gaba." Ma'aikatar a shiriritar nata, ta zargi fitacciyar kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya, Amnesty International, da laifin "tsoma baki a sha'anin dokoki da shari'ar Najeriya." Kila suna son a bar su da bin hanyar su ta keta da mugunta da sunan "dimokradiyya mai kawo ci gaba."

Sun nuna cewa wai sun daukaka karar hukuncin kotun da ta yi umarni da sakin Shaikh Zakzaky. Amma kuma sun ki bin umarnin kotun su sake shi din duk da cewa babu wata dokar dakatar da wancan hukuncin. Don kawai an shigar da karar daukaka hukuncin wata kotu, ba zai zama hujjar a ki bin umarnin ta ba, ba tare da cewa kotun daukaka karar ce ta dakatar ko jinginar da wancan hukuncin ba. A wannan lokacin dai babu wanda aka yi.

A bayyane yake, Ma'aikatar na fadin haka ne saboda gwamnati ta rasa hujjar ci gaba da musgunawa IMN tare da tsarewa ba bisa ka'ida ba da take yi wa Shaikh Zakzaky.

Wannan martani na kin gaskiya da gwamnati ta yi wa rahoton Amnesty International lallai abin tsoro ne. Ya kamata gwamnatin ta gane cewa babu wata farfaganda, bata suna da kuma yada karya a kan Harkar Musulunci da kuma Jagoranta da zai iya ba da hujjar kisan kiyashin da ya faru a Zaria, da kuma hana mu ’yancinmu na aikata addini bisa fakewa da kowane irin abu. Muna ba ta shawarar ya kamata ta karbi laifin kuskurenta, sannan kuma ta bi hanyar gaskiya da adalci. Sai bayan ta yi haka ne duniya za ta yarda da dimokradiyya mai neman kawo ci gaban da take ikirari.

Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA 
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya 
05/03/2017
Skype: Ibrahim.musa42


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky