Martani Gwamnatin Buhari Ga Obasanjo

Martani Gwamnatin Buhari Ga Obasanjo

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani dangane da kiran da tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari na cewa kamata ya yi ya je ya huta kada ya tsaya takara a zaben 2019.

A martanin da gwamnatin kasar ta mayar cikin wata sanarwa da ministan yada labarai na kasar, Lai Mohammed, ya fitar ya yi fatali da kiran yane mai kare gwamnatinsu da cewa ta samar da ci gaba a fanonnin da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar boko haram da kuma farfado da tattalin arziki.

Sanarwar ta ce batun tsayawa takara a zabe mai zuwa ta shugaba Buhari zata iya raba hankalinsa, a daidai lokacin da ya natsu wajen cikawa 'yan kasar da suka zabe shi a 2015 al'akawari.  

A ranar Litinin data gabata ce Obasanjo ya shawarci Buhari da cewa kamata ya yi ya je ya huta a 2019 saboda yawan shekarunsa da yanayin lafiyarsa, kiran da ya jawo kace nace ba kadan ba a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky