Manyan Kasashe Masu Arzikin Gas A Duniya Sun Soki Takunkuman Bangare Guda Na Amurka

Manyan Kasashe Masu Arzikin Gas A Duniya Sun Soki Takunkuman Bangare Guda Na Amurka

Kungiyar manya -manyan kasashe masu arzikin iskar gas a duniya sun yi Allah wadai da takunkuman bangare guda na gwamnatin kasar Amurka kan kamfanonin kasashen kugiyar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wakilan kasashen a taronsu na kasar Bolivia a jiya jumma'a suna sukar matakan da gwamnatin Donald Trump ta dauka na dora takunkumai kan kamfanonin hakar iskar gas na wasu kasashe membonin kungiyar, Kasashen kungiyar kasashe masu arziki gasa dai  13 ne wadanda sun hada da Rasha, Iran da kuma Venezuela. Sai kuma kasashe masu sanya ido a kangiyar wadanda suka hada da Kazakistan, Nethalanda, Norway da Iraqi. 

Gwamnatin Trump ta Amurka ta dorawa kamfanonin gas na kasar Rasha takunkumai wadanda suka haramta masu aiki a fagen shimfida bututan gas a kasashen turai. Har'ila yau tana barazanar dorawa kasar Venezuelan irin wadannan takunkuman, a yayin da take shirin maida takunkuman da ta dorawa Iran kafin yarjejeniyar 2015 tsakanin Iran da kasashe 5+1 wanda ya hada har da ita Amurkan. Kasar Rasha ne take bin Amurka a yawan arzikin gas a duniya. a


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky