Majalisar Wakilan Nigeria Ta Fara Bincike Kan Kisan Yan Nigeria 97 A Bakasin Kamaru

Majalisar Wakilan Nigeria Ta Fara Bincike Kan Kisan Yan Nigeria 97 A Bakasin Kamaru

A jiya Jumma'a ce majalisar wakilan Nigeria ta fara bincike don gano yadda jandarmari na kasar Kamaru suka kashe yan Nigeria 97 a yankin bakasi daga kudu maso gabacin kasar

Shugaban majalisar wakilan tarayyan Nigeria Yakubu Dogara ya fadawa jaridar Vanguad ta kasar kan cewa majalisarsa ta fara bincike dangane da labari mai cewa jami'an tsaron Jandarmari na kasar kamaru a yankin bakasi sun kashe yan Nigeria 97 a makon da ya gabata.

Dogara ya kara da cewa bayan bincike, majalisarsa za ta san yanda zata tunkari hukumomin kamaru kan lamarin  don kare hakkokin yan Nigeria da suke zaune a tsibirin na Bakasi.

Babatunde Kolawole, dan majalisar da ya gabatar da bukatar binciken a gaban majalisar a jiya jumma'a ya bayyana cewa akwai rahotanni daga kafafen yada labarai da dama kan cewa Jandarmari na kasar Kamaru sun kashe yan Nigeria 97 a yankin bakasi  bayan da suka kasa biyan N100,000 taran da aka ci su sanadiyyar kamun kifi a yankin. 

Dan majalisar ya kara da cewa akwai irin wadanda batutuwan kisan yan naigeria a yankin da  ke ta faruwa wadanda ba'a ji. A halin yanzu dai shugaban majalisar ya mika batun ga komitin harkokin waje na Majalisar don gudanar da cikekken bincike kafin majalisar ta san matakin da zata dauka a gaba.288 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky