Majalisar Tarayyar Afrika Ta Soki Halin Ko In Kula Na MDD Ga Nahiyar Ta Afrika

Majalisar Tarayyar Afrika Ta Soki Halin Ko In Kula Na MDD Ga Nahiyar Ta Afrika

Majalisar dokokin tarayyar Afrika ta soki halin ko in kula wanda majalisar dinkin duniya take nunawa nahiyar Afrika.

Tashar radiyo suwahili a nan Iran ta nakalto rahoton bayan taro na majalisar dokokin tarayyar ta Afrika ya na fadar haka bayan kammala wani taron da majalisar ta gudanar a birnin Kigali na kasar Ruwanda a jiya Litinin.

Rahoton ya kara da cewa yan majalisa 275 ne daga kasashe 55 na nahiyar suka halarci taro na farko na majalisar dokokin tarayyar na biyar. 

Batutuwan da yan majalisar suka tattauna a kai dai sun hada da yaki da ayyukan ta'addanci da kuma cin hanci da rashwa a kasashen Afrika. 

Shekaru 14 da suka gabata ne aka kafa tarayyar Afrika da nufin kyautata rayuwar mutanen nahiyar, amma masana suna ganin ci gaban da aka samu tun lokacin kafa tarayyar suna tafiyar hawainiya.

A karshen taron majalisar ta tarayyar Afrika ta bawa marigayi Kofi Anan tsohon babban sakataren MDD lambar girmamawa ta "iya harkokin gudanarwa"


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky