Majalisar Dokokin Kasar Libya Ta Bukaci Ganin An YI Fada Da Ayyukan Ta'addanci

Majalisar Dokokin Kasar Libya Ta Bukaci Ganin An YI Fada Da Ayyukan Ta'addanci

Majalisar kasar ta Libya ta bakin shugabanta Akilah Salih Isa ta mayar da martani akan harin ta'addancin da aka kai a yankin Ka'am a yammacin kasar.

Shugaban majalisar dokokin kasar ta Libya ya bayyana wajabcin samar da hadin kai a tsakanin dukkanin cibiyoyin tsaro na kasar da su ka hada 'yan sanda da jami'an tsaro na ciki, da kuma sojoji domin kalubalantar ta'addanci.

Kasar ta Libya ta fada cikin matsalar tsaro tun 2011 bayan kifar da gwamnatin Mua'mmar kaddafi.  Kungiyoyin ta'addanci irin su alka'ida da Da'esh sun mamaye wasu yankuna na kasar ta Libya tare da kai hare-haren ta'addanci a cikin sassan kasar daban-daban.

 Tun dai ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Libya ta sanar da kame wasu mutane uku da suke da alaka da kai harin ta'addancin Ka'am da ke tsakanin garuruwan Zalitan da Khums a yammacin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky