Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ta Ki Amincewa Da Bellewar Yankin Kurdawan Kasar Da Babban Rinjaye

Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ta Ki Amincewa Da Bellewar Yankin Kurdawan Kasar Da Babban Rinjaye

A yau talata ce majalisar dokokin kasar Iraqi ta kada kuri'ar rashin amincewa da zaben raba gardama wanda gwamnatin lardin Kurdawa na kasar suka kuduri anniyar gudanarwa a karshen wannan watan

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa majalisar ta ki amincewa da shirin sannan ta bawa Priministan kasar Haidar Abadi damar daukar duk matakin da yaga ya dace don hana bellewar yankin kurdawa daga kasar ta Iraqi.

Labarin ya kara da cewa wakilan kurdawa a majalisar sun fice daga zauren kada kuri'ar a lokacinda aka gabatar da batun, amma duk da haka majalisar ta yi watsi da bukatar bellewar da babban rinjaye.

Gwamnatin Yankin Kurdawa na kasar Iraqi dai ta kuduri anniyar gudanar da zaben raba gardama a yankin don shelanta bellewar yankin daga kasar ta Iraqi a ranar 25 ga wannan watan.

A cikin watan da ya gabata ne gwamnatin kasar Iraqi ta kawo karshen mamayar da kungiyar yan ta'adda ta Daesh ta yiwa wasu yankuna na kasar, sai kuma ga batun ballewar kurdawan kasar ya kunno kai, wanda masana suna ganin yakin da za'a yi da kurdawa sai ya fi na Daesh.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky