Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Cewa: Kananan Yara Fiye 1400 Ne Aka Kashe A Yamen

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Cewa: Kananan Yara Fiye 1400 Ne Aka Kashe A Yamen

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kan bil-Adama ya sanar da cewa: Akalla kananan yara 1400 ne aka kashe sakamakon hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.

Stephen O'Brien mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kan bil-Adama ya bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da irin da ake kai wa kan kasar Yamen sun yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da suka hada da kananan yara da yawansu ya haura 1400.

Stephen O'Brien ya kara da cewa: Kashi daya cikin uku na al'ummar Yamen da yawansu ya kai miliyan 19 a halin yanzu haka suna cikin matsanancin hali tare da bukatar tallafin gaggawa. Kamar yadda Asusu tallafa wa mata da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya fitar da rahoton cewa: Akwai kananan yara kimanin 500,000 da suke fuskantar matsalar masifar yunwa da rashin tsabtaceccen ruwan sha a kasar ta Yamen.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ne kasar Saudiyya da kawayenta suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen, inda a halin yanzu haka suka kashe mutane fiye da 11,000 tare da tilastawa wasu fiye da miliyan uku tserewa daga muhallinsu, baya ga rusa duk wani abu mai amfani a kasar ta hanyar hare-haren jiragen saman yaki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky