Limamin Tehran: Wajibi Ne Al'ummar Musulmi Su Yi Tsayin Daka Wajen Kalubalantar Makiya

Limamin Tehran: Wajibi Ne Al'ummar Musulmi Su Yi Tsayin Daka Wajen Kalubalantar Makiya

Limamin juma'ar ya yi wa al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w.)

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya yi kira ga musulmi sunna da shi'a da suka kama hannuwan juna su fuskanci makiyan al'uumar musulmi, tare da yin tsayin daka da kuma gwagwarmaya.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya kara da cewa; Bai kamata shi'a da sunna su bari makiyan musulunci su yaudare su ba, domin ba su yarda da hadin kai a tsakanin musulmi ba.

Ayatullahi Karmani ya yi ishara da  nasarar da aka samu akan kungiyoyin 'yan ta'adda tare da cewa hakan alkawali ne na Allah ne.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky